Gamayyar Ƙungiyoyin Ma’aikata Sun Yi Tir Da Lalata Kadarorin Gwamnati

Gamayyar Ƙungiyoyin Ma’aikata sun yi tir gami da Allah wadai da kone-kone gami da sace-sace da lalata Kadarorin Gwamnat, da na sauran jama’ai da ya gudana a Jihar Legas da sauran jihohin dake yankin Kudancin kasar.

Bisa ga haka gamayyar ƙungiyoyin ta yi kira da babbar murya ga Shugaban ƙasa Buhari, da ya gaggauta ɗaukar matakan da suka dace wajen tsaron lafiya da dukiyoyin jama’ar kasar.

Hakazalika Gamayyar Ƙungiyoyin sun yaba wa wadanda suka suka gudanar da Zanga-Zangar Endsars cikin lumana a fadin kasa, da kyakkyawar manufa inda suka yi fatan sauran masu Zanga-Zangar da ɗaukar darasi.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun Shugabannin Gamayyar Ƙungiyoyin da suka haɗa da Dr Banjo Ayodele na kungiyar Human Rights Advocacy, sai Madam Ngozi Okocha daga Conference Of Africa Mothers Forum, sai Hajiya Zainab Alƙali daga Justice And Equity Network da Barista Festus Igbokwe na Ƙungiyar Justice And People’s Network.

“Muna kira ga Shugaban ƙasa da ya samar da kyakkyawar tsaro a ƙasa, sannan muna kira ga gwamnoni da suyi gaggawar shirya zama da matasan Jihohin su domin samun bakin zaren.

Gamayyar ƙungiyoyin waɗanda suka bayyana cewar ko shakka babu matasan da suka mayar da hankali wajen kone-kone da satar kayayyakin jama’a ba sa daga cikin ainihin matasa wadanda ke gudanar da Zanga-Zangar Endsars, bisa ga haka suka nemi doka ta yi aiki a kan su.

“Babu kasar da zata cigaba a duniya a halin da aka wayi gari matasa na aika-aika a cikin ta, saboda haka ya zama wajibi a yi wa tufkar hanci”.

“Najeriya kasar mu ce gaba ɗaya ya zama wajibi mu yi kishin ta, ba kuma zamu rungume hannu muna kallon wasu bata gari na burin jefa kasar cikin mawuyacin hali.

Labarai Makamanta