Fyaɗe: Zamu Samar Da Dokar Ɗaurin Rai-Rai – Majalisa

Majalisar dattawa a yau Talata, 14 ga watan Yuli ta samar da sabuwar dokar daurin rai-da-rai ga duk wanda aka kama da laifin garkuwa da mutane a Najeriya, The Punch ta ruwaito.

Majalisar ta yanke shawarar canza dokar ne daga daurin shekaru 10 a gidan gyara hali zuwa daurin rai-da-rai.

Dokar wacce Sanata Oluremi Tinubu, ta shigar na da take “Bukatar canza dokar laifi CAP. C.38 na dokokin tarayyar Najeriya 2004.”

Hakazalika, dokar ta canza tsarin cewa wajibi duk wacce aka yiwa fyade ta kai kara cikin wani takaitaccen lokaci na watanni biyu, ko a karyata ta.

Bayan haka, an sauya tsarin cewa mata kadai ake yiwa fyade, yanzu dokar ta hada da maza.

A yanzu, komin dadewa da yiwa mutum fyade, zai iya shigar da kara kuma a saurara.

Yanzu za’a tura dokar majalisar wakilai domin su amince da dokar kafin kaiwa shugaban kasa ya rattafa hannu.

Laifukan garkuwa da mutane da fyade sun zama ruwan dare a cikin al’ummar Najeriya, daga kudu zuwa Arewa, babu inda ba’ayi.

Fari da laifin garkuwa, an sace daruruwan mutane a hanyoyin Najeriya, a gidajensu, a gonakinsu, a wuraren aikinsu, da sauran su.

Sabanin yadda aka saba a baya na sace masu hannu da shuni, yanzu abin ya game kowa har talaka bawan Allah bai tsira ba.

Hanyoyin da garkuwa da mutane ya fi yawaita a Najeriya sun hada da hanyar Abuja zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Zariya, Abuja zuwa Lokoja, Kaduna zuwa Birnin Gwari, Lokoja zuwa Okene, dss.

Kawo yanzu an damke daruruwan matasan da ke aikata wannan aika-aika kuma suna gurfana a kotu.

Daga cikinsu akwai manya irinsu Evans, da Hamisu Wadume.
Hakazalika laifin fyade ya zama ruwan dare musamman zakkewa kananan yara maza da mata.

Cikin yan kwanakin nan, an samu mahaifi ya yiwa diyar cikinsa fyade, kato ya zakkewa jaririya, da yiwa luwadi da kananan yana musamman Almajirai.

Labarai Makamanta

Leave a Reply