Fitintinu: Sarkin Musulmi Ya Ayyana Juma’a Ta Zama Ranar Addu’a Ta Musanman

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta shari’ar Musulunci a Najeriya (NSCIA), Alh Muhammad Sa’ad Abubakar, ya alanta ranar Juma’a matsayin ranar addu’a ta musamman ga Najeriya.

Sarkin ya umarci Musulman Najeriya su yi addu’a bisa rikicin da yayi sanadiyar asarar rayuka da dukiya a yankin Arewa da Legas, Benin da wasu jihohi.

Mai Alfarma ya jaddada cewa addu’a da komawa ga Allah kadai ya rage a yiwa kasar nan domin samun zaman lafiya.

Sarkin Musulmi a jawabin da ya saki a Abuja ranar Laraba, ya bukaci dukkan Limamai su yi Khuduba kan rikicin dake faruwa a kasar domin kwantar da hankalin mabiya.

Ya ƙara da ceea duk wanda yayi imani da Allah, babu matsalar da ba zata iya magantuwa da addu’a ba. Hakazalika Sarkin Musulmi ya bukaci Musulmai ‘Yan Najeriya dake kasashen wajen su sa baki wajen addu’a.

Labarai Makamanta