Fitinar ‘Yan Bindiga: Masarautar Katsina Ta Soke Bikin Hawan Sallah

Mai Martaba Sarkin Katsina, Alhaji Abdulmuminu Kabir Usman ya ba da sanarwar dakatar da bikin hawan Babba Sallah wadda aka saba yi duk shekara, biyo bayan hare-haren ‘yan bindiga da suke kaiwa a wadansu yankunan jihar Katsina da kuma wannan cuta ta Covid 19, Wanda har zuwa yanzu akwai burbushin ta a jihar Katsina.

Bayanin hakan na kunshe, a cikin wata takarda da Sakataren Masarautar Katsina, Alhaji Bello Mamman Ifo ya sanyawa hannu.

Sanarwa ta kara da cewa Mai Martaba Sarkin Katsina, ya umurce ni sakamakon hare-haren da yan bindiga ke kaiwa, wanda ya yi sanadiyyar rasa rayukan al’ummar jihar Katsina da dukiyoyi da kuma iftila’in cutar Corona. Don haka Mai Martaba Sarkin Katsina yan majalisar sa ta zauna ta yanke shawarar ba za’a samu gudanar da hawan Babba Sallah ba, domin zaunawa taya jimamin rashe-rashen da al’umma suka yi, da kuma wannan cutar wanda har zuwa yanzu akwai burbushin ta a jihar Katsina.

Annobar ‘Yan BindigaDon haka Mai Martaba Sarkin Katsina, ya yi kira da al’ummar Masarautar Katsina, su zauna gida a cigaba da yin adduar samun zaman lafiya a jihar Katsina da Nijeriya baki daya.

Labarai Makamanta

Leave a Reply