Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake tabbatar wa Gwamnonin Arewa cewa gwamnatin sa za ta kawo karshen matsalar tsaro a Arewa, matsalar kuwa ko ma wace iri ce.
Gwamnonin Arewa sun kai wa Shugaba Buhari wannan ziyara ce bisa jagorancin Shugaban Kungiyar Gwamnaonin Arewa, Simon Lalong na Jihar Filato.
A wannan ganawar da ya yi da su ne a ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya sake sha masu alwashin kawo karshen dukkan matsalolin tsaro a Arewa baki daya.
Sun yi wannan ganawar ce a ranar da aka yi jana’izar mutum kusan 80 da ‘yan bindiga su ka kashe a garin Magami, cikin Jihar Zamfara.
Wadanda su ka halarci ganawar sun gada da Shugaban Kungiyar Gwamnonin Arewa, Simon Lalong na Jihar Filato, Governor Simon Lalong, Gwamnan Kebbi, Atiku Bagudu; Kaduna, Nasir El-Rufai; Yobe, Mai Mala-Buni, Niger, Abubakar Bello; da Nasarawa, Abdullahi Sule.
A wurin ganawar akwai Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.
A taron dai gwamnonin sun rika yin magana daya bayan daya dangane da kokarin da kowanen su key i wajen ganin an samar da tsaro a jihar sa, tare kuma da neman abin da ya ke bukata gwamnatin tarayya za ta yi a kan lamarin.
Da ya ke magana da manema labarai bayan tashi daga taron a Fadar Shugaban Kasa, Lalong bayyana masu cewa Shugaba Buhari na da yakinin ganin ya kawo karshen matsalar tsaro a kasar nan.
Ta kara jaddada masu cewa babu wani batu da su ka tattauna da Shugaba Buhari baya ga na matsalar da ta fi damun Arewa, wato matsalar tsaro.