Fitar Buhari Da Osinbajo: ‘Yan Najeriya Sun Shiga Rudanin Rashin Sanin Jagora

‘Yan Najeriya sun shiga cikin ruɗani na rashin sanin ko wanene ragamar ƙasa take a hannunsa yanzu biyo bayan ficewar Buhari da mataimakin sa Osinbajo daga kasar.

Idan jama’a za su tuna Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya cilla birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron majalisar ɗinkin Duniya karo na 77, yayin da Osinbajo ya garzaya Ingila domin shaida jana’izar Marigayiya Sarauniyar Ingila Elizabeth ll.

A halin da ake ciki yanzu dai za a iya cewa babu jagora da ke riƙe da ragamar shugabancin Najeriya kasancewar Shugaban da mataimakin nashi sun yi nuƙusani.

Duk da yake a tsarin kundin mulki ya shar’anta cewa idan Shugaba da mataimakin shi ba sa nan to jagorancin ƙasa zai koma hannun Shugaban Majalisar Dattawa ne, amma abin da jama’a ke korafi akai shine Buhari bai sanar da hakan a hukumance ba idan har ma yin hakan ya tabbata.

‘Yan Najeriya da dama da aka zanta dasu sun nuna takaici da damuwarsu akan haka, inda suke ganin rashin martaba ƙasa da dokokin kasar ne ya sanya Shugaba da mataimakin shi suka fice suka bar ƙasa babu tsari na jagoranci.

Labarai Makamanta

Leave a Reply