Fina-Finai: Ina Nan Da Raina Ban Mutu Ba – Kamaye


A safiyar ranar jiya ne wani labari ya karade shafukan sada zumunta ana fadin cewa Allah yayiwa fitaccen Marubucin nan kuma darakta haka kuma a lokaci daya jarumi a masana’antar kannywood Dan Azumi Baba wanda akafi sani da Kamaye rasuwa.

Jaruman Kannywood da dama sun wallafa hakan,wasun su sun karyata kansu daga baya,yayin da wasu kuma suka cire wallafar ba tare da bada wani ba’asi ba.

Bayan mun gudanar da bincike ne muka tabbatar muku da cewa yana nan a raye cikin koshin Lafiya.

Haka kuma shima jarumin da kansa ya fito ya karyata hakan a shafinsa na Instagram: “Ina nan a raye ban mutu ba da sauran shan ruwa, masu yaɗa labarin na mutu suyi hakuri lokaci bai yi ba tukuna”

Labarai Makamanta

Leave a Reply