Filato: Zanga-Zangar SARS Ta Rikiɗe Rikici

Zanga-Zangar #EndSARS da ake gudanarwa a garin Jos, babbar birnin jihar Filato, ta kaure ta zama rikici, bayan da wasu ɓatagarin Matasa suka sauya salon tafiyar Zanga-zangar zuwa wani abu na daban.

A cewar rahoton, an samu tashin hankali a hanyar Ahmadu Bello Way da ke garin Jos yayinda masu zanga-zanga suka sanya shingaye a babban titin da ke sada mutum da cikin birnin a ranar Talata, 20 ga watan Oktoba.

A kan haka, wasu matasa sun samu sabani da wadanda suka sanya shingen, wanda hakan ya haifar da tashin hankali. An farfasa motoci da yawa sannan aka kona wasu, an kuma lalata shaguna.

An tattaro cewa an rufe harkoki a birnin domin hana ci gaban barnar. An kuma jiyo karar harbe-harben bindiga a yankin, lamarin da ya tursasa mazauna yankin barin wajen.

A halin yanzu, an turo jami’an tsaro domin kwantar da tarzoman.

Labarai Makamanta

Leave a Reply