Filato Ta Zama Cibiyar CORONA A Najeriya – Fadar Shugaban Ƙasa

Kwamitin Shugaban ƙasa mai yaƙi da cutar CORONA ya ce cutar ta yi kamari a Jihar Filato. A halin yanzu an yi kwanaki biyu a jere Filato ta na zama kan gaba a jihohin da ake samun bullar Coronavirus.

Shugaban kwamitin da shugaban kasa ya kafa domin yaki da annobar COVID-19, Boss Mustapha ya bayyana cewa Filato ta sha gaban kowace jiha a yau, ta zama abin damuwa.

A baya jihohi irinsu Legas, Kano, Ogun da Oyo ne cutar ta yi kamari. A ‘yan kwanakin nan, alkaluma sun tabbatar babu inda ake samun bullar COVID-19 irin jihar Filato.

Mista Mustapha ya yi wannan jawabi ne a madadin kwamitin a lokacin da ya zanta da ‘yan jarida a jiya. Ya ce: “Yayin da mu ke shiga makon karshe na takunkumin da aka tsawaita, da la’akari da raguwar wadanda su ke mutuwa da karancin masu kamuwa da cutar, PTF za ta ja hankalin mutane game da canjin da aka samu a yaduwar cutar.”
“Za mu tuna cewa Legas, Kano, da Ogun ne da inda cutar ta yi kamari, daga nan ta koma Oyo a wani lokaci, yanzu abin ya koma Filato.” inji Mustapha.

Sakataren gwamnatin tarayya ya ce kamar yadda kwamishinan lafiya na Legas, Akin Abayomi, ya fada, ana samun sa’ida a jihar, amma hakan ba ya nufin an kawo karshen annobar ba.
“Burinmu shi ne mu yi wa dinbin mutane gwaji a fadin kasar nan.” Inji shugaban kwamitin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply