Filato: Rikicin ?abilanci Ya ?arke A Jos Babban Birnin Jihar

Rahotanni daga Bukur na ?aramar Hukumar Jos ta Kudu a Jihar Filato na cewa ana arangama tsakanin ?abilun yankin.

Mazauna yankin sun shaida wa BBC cewa yanzu haka jami’an tsaro na harbi a sama domin tarwatsa matasan da ke jefe-jefe da duwatsu.

Mai magana da yawun ‘yan sandan Jihar Filato Uba Gabriel bai tabbatar da faruwar lamarin ba amma ya ce zai bincika.

An fara rikicin ne tsakanin al’umma Hausa/Fulani da kuma sauran ?abilun yankin bayan zargin juna da fara aikata kisa.

Jihar Filato da ke sashin Tsakiyar Arewacin Najeriya ta kasance wata jiha wadda ta da?e tana fama da rikice-rikicen ?abilanci da na addini, lamarin da ke haifar da asarar dukiya da rayukan jama’a.

Related posts

Leave a Comment