Gwamnatin Jihar Filato ta haramta Sallar Idi a jihar a bana yayin da adadin mutanen da suka kamu da cutar a jihar ya kai 982.
Gwamnan jihar kuma Shugaban kwamitin yaki da COVID-19 na jihar, Gwamna Simon Lalong ne ya sanar da haramcin yayin jawabin da ya yi wa manema labarai kan matakan da jihar ke dauka kan annobar a ranar Talata a Jos.
Gwamnan ya kuma haramta duk wasu bukukuwa da aka saba yi da sallah da suka hada da ziyartar wuraren shakatawa da gidajen dabobin namun daji da sauransu.
“Dukkan mazauna jihar suyi amfani da takunkumin fuska, musamman yara a lokacin da suke kai wa yan uwa da abokan arziki abinci,” in ji shi. Mr Lalong ya ce hakan ya zama dole ne bayan karuwar adadin masu cutar da aka samu a jihar tare da bikin sallar da ke karatawo domin dakile yaduwar cutar.
Mr Lalong ya kuma tunatar da mazauna jihar game da dokar takaita fita da gwamnatin tarayya ta saka na karfe 4 na asuba zuwa 10 na dare tana nan tana aiki. Ya ce an samu karuwar mutanen da suka kamu da cutar a jihar saboda akwai dakin gwaje gwaje guda uku a jihar:
Cibiyar Binciken Dabobbi ta Kasa da ke Vom; Asibitin Kwararru da ke Plateau da Asibitin Koyarwa na Jami’ar Plateau.