Fetur A Arewa: An Soki Tinubu Na Yin Watsi Da Aikin Jihohin Bauchi Da Gombe

IMG 20240225 WA0030

Kungiyar RDI ta yi tattakin jin halin da al’ummar yankin Kogin Kolmani suke ciki, tun bayan ayyaka samun ɗanyen man fetur da kuma gas a yankin da gwamnatin tarayya ta yi a cikin 2022.

RDI ta nuna ɓacin rai ga Gwamnatin Tarayya, ganin cewa har yanzu ba ta fara shirin komai ba dangane da ɗaukar matakai da kuma sanar da al’ummar yankin Kolmani irin illolin da ayyukan haƙar ɗanyen mai kan haifar ga mazauna yankin da ake haƙo man.

ɓacin rai na RDI ta bijiro ne bayan da ƙungiyar ta yi zaman tattaunawa domin jin ta bakin mazauna yankin a cikin Ƙaramar Hukumar Alƙaleri ta Jihar Bauchi, a ranar 28 ga Fabrairu, 2024.

A wurin jin ta bakin mazauna yankin, sun samu ƙarin ilmin sanin matsaloli da Illolin da ka iya shafar su idan aka fara haƙar ɗanyen mai a yankin. An buga masu misalai da irin ibtila’o’in gurɓacewar muhalli da yankin Neja Delta mai arzikin man fetur ke fuskanta.

Mazauna yankin na Kolmani sun shaida wa RDI cewa babu wani ƙarin haske da suka samu daga Gwamnatin Tarayya.

Sannan kuma yankin na fuskantar rashin jituwa tsakanin mazauna daga jihohin Bauchi da kuma Gombe, inda kowane ɓangare ke iƙirarin yankin su aka ce an samu ɗanyen mai ɗin.

Sannan kuma sun yi kuka dangane da yadda ake ci gaba da fuskantar matsalar tsaro a yankin, sai kuma yawan gilmawar baƙin da ba a san ko daga ina suke ba, tun bayan ayyana samun ɗanyen mai a Kolmani.

Tun a cikin watan Oktoba, 2019 ne dai Gwamnatin Tarayya ta ayyana cewa akwai ɗanyen mai har ganga biliyan 1 da kuma kubik biliyan 500 na gas a kwance a ƙarƙashin yankin Kolmani, wanda ya mamaye jihohin Bauchi da Gombe.

An damƙa aikin haƙar rijiyoyin ɗanyen mai ɗin ga kamfanin Global Oil, Hukumar Raya Yankin Arewa maso Gabas, NNDC da NNPC. Kuma har zuba jarin Dala biliyan 3.

Sai dai kuma babu wani abin da Gwamantin Tarayya ta yi, run bayan rakaɗi da kwakwazon bayyana an samu ɗanyen mai a yankin. Gwamnati ba ta sanar wa mazauna yankin barazanar dagwalon masana’antu mai haifar da illollin gurɓacewar muhalli.

Babbar Jami’ar Gudanarwar Ayyuka ta RDI, Ifeoluwa Adediran, ta ce: “Ko kaɗan ba daidai ba ne bayan gwamnatin tarayya ta cika duniya da giringiɗishin samun ɗanyen mai, sai kuma ga shi har yau babu wani hoɓɓasa da aka yi domin janyo hankalin mazauna yankin. Sai dai kawai ana yaudarar su ana sanar da su muhimmancin samun ɗanyen mai a yankin su.”

Ta ce yanzu haka siyasa ta shiga cikin shirin samar da ɗanyen mai ɗin, inda mutane da dama ke ci gaba da nuna hannu cikin batun alherin da za a samu a yankin.

RDI ta ce za ta ci gaba da wayar wa mutanen yankin kan su domin su san haƙƙoƙin su da ‘yancin su da kuma abin da ka iya taso masu idan aka fara haƙar ɗanyen mai a yankin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply