Wani kwararren Lauya mai suna Iheanacho Agboti da ke aiki a garin Abakaliki, jihar Ebonyi, ya yi magana a game da rikicin kungiyar ASUU da jami’ar FUTO dangane da batun ba minista Pantami mu?amin Farfesa.
Barista Iheanacho Agboti ya ce a dokar aikin kasa wanda aka yi wa garambawul a shekarar 2005, babu yadda ASUU ta iya da jami’ar. Masanin shari’ar ya ce dokar Trade Union (Amendment) ta 2005 ba ta ba kungiyar ASUU hurumin ta hukunta shugabannin jami’a idan su ka saba wata doka ba.
Lauyan ya bayyana wannan ne da yake magana da ‘yan jarida a garin Abakaliki domin yin karin haske a kan abin da doka ta ce a game da surutun da ake ta yi.
Barista Iheanacho Agboti ya caccaki kungiyar malaman jami’ar da shiga hurumin da ya fi karfinta. A cewarsa, majalisar da ke sa ido a kan harkar jami’a ce kadai dokar Universities Miscellaneous Provisions Act 2012 ta amince ta hukunta shugabannin jami’a.
“Ni Lauya ne, kuma gaskiya ita ce ASUU ba ta da hurumi a dokar ‘Nigerian Trade Union’ da za ta dauki mataki a kan shugabannin jami’ar FUTO a kan zargin saba doka.” “Jahiltar gaskiyar lamarin da ASUU ta yi abin takaici ne.