Farashin Mai Da Lantarki: Za Mu Tsunduma Yajin Aiki – ‘Yan Ƙwadago

Gamayyar manyan kungiyoyin kwadagon Najeriya na NLC da TUC, sun yi watsi da hukuncin kotun sasanta rikicin ma’aikata ta Najeriya, da ta haramta musu shiga yajin aikin gama gari, da kuma gudanar zanga-zanga a fadin kasar, da suka shirya jagoranta a ranar Litinin 28 ga watan Satumba, don adawada karin kudin litar mai da lantarki.

Kungiyoyin kwadagon sun lashi takobin aiwatar da nufinsu ne a daren jiya Alhamis, bayan gaza cimma matsaya tsakaninsu da gwamnati, a taron da suka rabu baram baram

Bayan taron ne ‘yan kwadagon suka ce suna kan bakansu na shiga yajin aiki, gami da jagorantar zanga-zanga, har sai gwamnati ta janye Karin kudin man fetur da hasken wutar lantarki.

Yayin haramtawa ‘yan kwadagon soma ayjin aiki da zanga-zangar, Alkalin kotun Najeriyar dake sasanta rikicin ma’aikata Ibrahim Galadima, ya kuma baiwa Sifeto Janar na ‘Yan Sanda da shugaban hukumar DSS umurnin bada kariya ga duk wani ma’aikaci domin ganin yaje wurin aikinsa ba tare da tsangwama ba.

Labarai Makamanta