Farashin Mai Da Lantarki: Ƙungiyar Ƙwadago Ta Sanya Ranar Zanga-zanga

Kungiyar Kwadago ta Kasa, NLC, ta ce ba za ta fasa zanga zangar da ta shirya yi ba daga ranar 28 ga watan Satumban 2020 bayan gwamnatin tarayya ta ki mayar da tsohon farashin man fetur da lantarki a kasar.

Kwamared Wabba ya ce dukkannin shugabannin kungiyoyin na jihohin Najeriya 36 da na Abuja sun amince da fara yin zanga-zangan daga ranar 28 ga watan Satumba.

Ayuba Wabba ya ce kungiyar za ta gudanar da zanga-zangar da ta shirya yi mako mai zuwa bayan fitowa daga taron Majalisar Zartarwar Kungiyar da aka yi ranar Talata a Abuja.

Ya ce shugabannin jihohi 36 na kungiyar da na Abuja dukkansu sun amince da yin zanga-zangar kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Labarai Makamanta

Leave a Reply