Rahotannin dake shigo mana daga Jihar Sokoto na bayyana cewa kwamitin duban wata na fadar mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya sanar da cewa ranar Laraba ita ce ɗaya ga watan Muharram, abin da ke alamta shiga sabon watan Musulunci.
Cikin wata sanarwa da kwamitin ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce bayan gaza ganin watan a ranar Talata, hakan ya sa wata cika kuma yau ɗaya ga watan Muharram.