Shugaban Dakarun Rundunar Sojin Najeriya Janar Tukur Yusuf Buratai, ya ce wasu ‘yan ta’adda na ta tsoratar da su da yunkurin hanasu fita kasashen ketare.
Tun bayan bude wutar da sojoji suka yi a Lekki Toll gate a Birnin Ikko a yayin Zanga-Zangar Endsars Jami’an rundunar suka shiga tsaka mai wuya.
A wani taro da shugaban rundunar sojin kasa, Tukur Buratai yayi a Abuja, ya zargi wasu kungiyoyi na kasashen ketare da tsoratar da Sojojin da fita kasashen waje saboda zargin shiga hakkin bil’adama.
“Ya ce wasu miyagu na tsoratar da mu da hana mu kara fita kasashen ketare, amma kada mu damu, domin wajibi ne zamanmu don gyara kasarmu,” cewarsa.
“Akaron farko da na fita kasar waje, na kai shekaru 50 kuma janar ne ni, don haka ban damu ba idan na karasa rayuwata a nan,”.
Wasu ‘yan Najeriya sun yi kira ga kasashen ketare da su dakatar da sojoji daga fita daga Najeriya sakamakon harbin masu zanga-zangar lumana da suka yi.
Buratai ya ce ba za su taba barin wani dan kasa ko kuma dan kasar waje ya cutar da kasa. Ya ce zai cigaba da iyakar kokarinsa wurin tabbatar da zaman lafiya a kasa.