EndSARS: ‘Yan Daba Sun Bankawa Sakatariyar Legas Wuta

Wasu da ake zargin ‘yan daba ne cikin masu Zanga-zangar SARS sun kone wasu gine-gine a cikin sakatariyar karamar hukumar Ajeromi na jihar Legas.

Sakataren watsa labarai na karamar hukumar, Sheriff Fakanle ya tabbatarwa wakilin The Punch afkuwar lamarin. Da aka tuntube shi misalin karfe 1.13 na rana, Fakunle ya ce ana cigaba da kai harin a sakatariyar karamar hukumar.

“A halin yanzu da na ke magana da kai, ‘yan daba dauke da makamai sun afka sakatariyar karamar hukuma ta. An lalata kayayyaki na miliyoyin naira. Wasu daga cikin ‘yan daban suna shiga ofisoshin mu, suna awon gaba da kayayyaki.

An kone gine-gine da motoci, matasa na sata a cikin sakatariyar.” Tunda farko, wasu matasa da ake zargin ‘yan daba ne sun kai hari ofishin ‘yan sanda da ke karamar hukumar Ifelodun sun banka masa wuta.

Kazalika wasu da ake zargin bata gari ne sun kona ofishin ‘yan sanda da ke Orile Iganmu duk a jihar Legas.

Labarai Makamanta

Leave a Reply