Ƙungiyar kafafen yada labarai masu zaman kan su a Arewacin Nijeriya, sun nuna matukar takaicin su, game da abubuwa da ke wanzuwa a Nijeriya, musamman zanga-zangar adawa da rundunar SARS, wadda aka fara cikin lumana, amma daga bisani ta rikide zuwa tarzoma, har ta kai ga ana banka wa kamfanoni da ma’aikatun gwamnati wuta, baya ga satar dukiyoyin al’umma, tare da salwantar da rayuka da dukiyoyin bayin Allah.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata takardar sanarwa wadda ta samu sanya hannun Shugaban ƙungiyar, kuma Shugaban Gidan Talabijin da Rediyo na Liberty Alhaji Ahmed Tijjani Ramalan, kuma aka rarraba ta ga manema labarai.
“Babban abin da ya fi damun mu shi ne, miyagun maganganun da ke fita dga bakunan wasu ‘yan Nijeriya, musamman ‘yan siyasa da manyan masu fada aji, dangane da bukatar masu rajin ganin an yi wa aikin ‘yan sandan Nijeriya da tsarin gudanar da harkokin gwamnati garambawul”.
Ƙungiyar kafafen yada labarai masu zaman kan sun a arewacin Nijeriya, sun lashin takobin ganin ta kowace fuska, ba su bada damar da wani zai yi amfani da su wajen bayyana duk wani abin da zai iya kasancewa barazana ga hadin kan kasar nan ba, domin babu wani abin da ya fi hadin kan ‘yan Nijeriya mahimmanci a halin yanzu, don haka, sun ce ba za su taba ba duk wani mai mummunar manufa damar yada farfagandar sa a kafafen su ba.
Sannan sun yi kira ga daukacin al’ummar Nijeriya da su yi hakuri da juna a kuma zauna a kan teburin tattaunawa domin fahimtar juna, sun kuma bukaci shugaba Muhammadu Buhari, ya gaggauta fitowa fili ya yi wa ‘yan Nijeriya jawabi, domin kawo karshen asarar rayukan bayin Allah da dukiyoyin da ake yi.
“Ya kai shugaban kasa, don girman Allah, ka hanzarta daukar matakin da ya dace, don gudun kada kasar nan ta fada cikin halin yaki da rashin kwanciyar hankali”.
” Anamu bangaren, muna baka tabbacin cewa za mu yi dukkan mai yiwuwa, ta fuskar ci-gaba da wayar da kawunan al’umma, game da kyawawan manufofin gwamnati, musamman a fannin labarai da rahotanni da sauran shirye-shirye, domin dinke duk wata barakar da ke neman zama barazana game da hadin kan kasar nan.
Muna rokon duk masu kafafen yada labarai su kauda duk wani nau’i na son zuciya, wajen sakin bayanai ko kuma labarai da rahotannin da za su wargaza ‘yancin da muka samu daga mulkin mallaka da kuma tsarin dimokaradiyyar mu.