EndSARS Shirine Na Ƙwace Mulki A Arewa – Miyyeti Allah

Wata kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah mai suna Kautal Hore, ta zargi tsohon gwamnan jihar Lagas, Asiwaju Bola Tinubu, da daukar nauyin zanga-zangar #EndSARS.

Miyetti Allah, a wani rahoto daga jaridar The Sun ta yi ikirarin cewa wasu ‘yan siyasa daga yankin kudancin kasar, ciki harda Tinubu, sune ke daukar nauyin zanga-zangar fadin kasar.

Kungiyar ta yi zargin cewa shirin domin dagulawa da tunkude gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ne da kuma son tsoratar da arewa don ta hakura da ‘yancinta na jagoranci har bayan 2023.

An ruwaito cewa hakan na kunshe ne a cikin wani jawabi dauke da sa hannun sakataren kungiyar, Alhaji Bello Bodejo da Alhasan Saleh.

Ƙungiyar ta dasa ayar tambaya kan dalilin da zai sa matasa su ci gaba da zanga-zanga da tayar da rigima bayan an cika burinsu na soke SARS.

Sai dai, Tunde Rahman, mai magana da yawun Bola Tinubu, yace babu gaskiya a zantukan da ke yawo na cewa yana daga cikin wadanda suka dau nauyin zanga-zangar EndSARS.

A wata takarda da ya fitar a ranar Asabar, Rahman ya ce Tinubu ba zai iya daukar nauyin zanga-zangar da za ta shafi tattalin arzikin jihar Legas ba. Ya kara da cewa, ba zai yiwuba jigo a jam’iyyar APC ya dauka nauyin zanga-zangar ba a duk jihohin da take faruwa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply