#EndSARS: Sai Mun Cire Bambance-Bambance Kafin ?asa Ta Zauna Lafiya – Bafarawa

Jigo a jam’iyyar PDP Alhaji Attahiru Bafarawa, ya ce idan har ‘yan Nijeriya ba zasu cire bambance-bambancen Addini ko jam’iyya ba, kasar ba zata taba zama lafiya ba.

Bafarawa ya kara da cewa idan kasar bata zauna lafiya ba, babu yadda za’ayi a gudanar da ibada cikin kwanciyar hankali, ko shugabancin kasar.

Duk wani musifan da zata fado kasar babu ruwanta da bambance-bambancen Jam’iyya ko wani abu akasin haka, kan kowa musifan zata fada.

Daga karshe ya yi kira ga al’ummar kasar da su kasance tsintsiya madaurin daya don ganin an kawo tashin tashin dake faruwa a kasar.

Related posts

Leave a Comment