EndSARS: Na Janye Saboda Ta Canza Salo – Jagoran ‘Yan Zanga-Zanga

Ɗan-gwagwarmaya, Segun ‘Sega’ Awosanya jagoran Matasa masu Zanga-Zangar SARS, ya sanar da janye hannunsa daga zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman na yaƙi da fashi da makami(#EndSARS) cikin gaggawa.

Ɗan gwagwarmaya ƴanchi, wanda ya jagoranci yaki da tozarci da muguntar ƴansanda a shekarar 2017 wanda kuma ya kasance jagaba a zangar-zangar kwanan nan, ya ce zanga-zangar ta sauya akala inda yace ma su wasu manufofi daban-daban sun ƙwace ragamar zanga-zangar.

A cikin wata hira da aka yi da shi, ya ƙara da cewa; “duba ga yadda ake kai hari ga manyan mutane da kuma amfani da wannan dama don samar da kuɗi ta hanyar ƙungiya mai zaman kanta wadda bata da sahalewar hukuma.

“Hakan gaskiya ya zama barazana ga tsaron ƙasarmu da kuma yunkurin mayar da matasanmu ƴan tawaye da sunan zanga-zangar kawo ƙarshen sashe na musamman mai yaƙi da fashi da makami (#EndSARS).

Shin wannan ba rashin hankali bane?” Sakamakon kai hare hare ga jami’an ‘yan sanda da fararen hula gwamnati ta kakaba dokar ta baci ta awanni 24 a jihar Legas.

Labarai Makamanta

Leave a Reply