Shugaban Kungiyar tuntuba ta hadaka ta Arewacin Nigeria (Arewa ConsultativeAndSynergyCongress) Engr Dr Harris yayi kira ga Gwamnatin Tarayya da sauran gomnatocin kudancin Nigeria da su bada kyakkyawar kulawa ga al’umman Arewa mazauna Kudancin Nigeria.
Engr Dr Harris Jibril ya kara da cewa al’umman Arewa mazauna Kudancin Najeriyar na fuskantar baraza wadda hakan zai iya tada hankalin jama’ar Arewa, daga ‘yan kudancin Nigeria masu zanga zangar neman a rushe rundunar yaqi da fashi da makami #SARS.
Al’ummar Arewa mazauna kudancin kasar nan sun duqufane wajen kasuwanci da sana’oin hannu da ayyukan kamfanoni, saboda haka suma suna bada muhimmiyar gudummuwa wajen habaka tattalin arzikin yankin da Najeriya baki daya, saboda haka suna buqatar a basu kyakkyawar kulawa domin kuwa sun dauki wani bangare na habaka tattalin arzikin kasa .
‘Yan Arewa mazauna Kudancin Nigeria suma ‘yan kasane kamar kowa, dan haka suna da buqatar a basu kyakkyawar tsaro, sannan suna da damar zama ako ina fadin kasarnan kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar mu ya bayyana ba tare da tsangwama ba.
Daga karshe Engr Harris Jibril yayi addu’ar samun zaman lafiya mai dorewa musamman a yankin arewa da kasar mu Najeriya.