EndSARS: Matasan Arewa Sun Soki Lamirin Kungiyar Amnesty

Gamayyar ƙungiyoyin Matasan Arewa 19 sun soki lamirin Ƙungiyar nan mai rajin kare haƙƙin ɗan Adam ta Amnesty bisa ga kwarmaton da take ta yi akan Harbe-Harben Lekki tare da kawar da kai akan matsalar tsaro da yankin Arewa ke fama dashi.

Gamayyar kungiyoyin matasan na Arewa sun bayyana hakan ne a yayin wani taron manema labarai da suka kira a gidan Tarihi na Arewa domin mayar da martani dangane da wata takarda da shugaban kungiyar Amnesty Mista Osai Ojigho ya fitar yana kalubalantar gwamnatin tarayya da yunkurin rufe gaskiyar abin da ya faru a Lekki.

Mai magana da yawun kungiyoyin matasan Abdul-Azeez Suleiman yace abin mamaki ne da takaici yadda Ƙungiyar Amnesty ke ƙoƙarin nuna bambanci a ayyukan kungiyar ta ƙoƙarin fifita wasu da mantawa da wasu.

Matasan sun koma nuna damuwar su akan matakan da kungiyar Amnesty ta dauka hadda shugaban ‘yan Sanda na ƙasa ta hanyar bada fifiko ga Zanga-Zangar Endsars ta Kudu da fatali da Endinsecurty ta Arewa.

“Ya kamata a gane cewar Zanga-Zangar Endsars an faro ta ne a cikin watan Oktoba daga yankin Kudancin Najeriya suna bukatar a soke rundunar SARS, amma Zanga-Zangar Endinsecurty an an faro ta ne wata huɗu da suka gabata, suna nuna damuwa da halin tsaro ya ke shiga arewa”.

Bisa ga haka gamayyar kungiyoyin suna kira ga kungiyar Amnesty da ta farka daga barcin da take ciki ta fuskanci abubuwan da ke addabar ƙasa ba wani yanki ba.

Sannan suna kalubalantar Amnesty da ta faɗada ayyukan da take hanƙoron yi zuwa ga yankin Arewacin Najeriya, inda ya dade yana fama da matsaloli na taɓarbarewar tsaro.

“Muna kuma gayyatar Ƙungiyar Amnesty da ta ziyarci yankin Arewacin Najeriya ba sashin kudu ba, sannan ta kasance mai gudanar da bincike ba nazari ba dogaro da labaran ƙanzon kurege ba. Domin batun kashe Kashen Lekki ko gwamnatin Jihar Legas ta musanta faruwar hakan”.

Daga ƙarshe matasan na Arewa sun tunatar da kungiyar ta Amnesty cewa, mutuncin su zai kasance ne kawai ga jama’a, idan ya zamana suna adalci akan ayyukan su.

Labarai Makamanta

Leave a Reply