EndSARS: Makomar Ƙasa Na Hannun Matasa Mu Tamu Ta Ƙare – Buhari

A ranar Litinin ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya sanar da matasan da ke zanga-zangar ENDSARS a kan cewa ganin damarsu ce su rungumi zaman lafiya, ko kuma akasin haka domin makomar su anan gaba.

Shugaban ƙasa Buhari ya yi wa matasa tunin cewa rayuwarsa da ta sauran sa’o’insa ta zo gangara, a saboda haka, zaman lafiya matasa zai fi yi wa rana.
“Mu tamu ta ƙare babu abin da ya sauran mana illa fatan cikawa da imani, saboda haka alkiblar makomar kasar na hannun ku ne Matasa”.

Shugaban ya fadi hakan ne yayin da ya karbi bakuncin mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya Hajiya Amina J. Mohammed, tsohuwar ministar muhalli a Najeriya, a fadar Shugaban ƙasa dake birnin tarayya Abuja.

A cewarsa; “alhakin matasa ne su rungumi zaman lafiya. Su na bukatar aiki da abubawan more rayuwa, fiye da kowa a kasar nan.
“Na aika shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Gambari, ya zagaya ko ina a kasar nan, ya tattauna da Sarakunan gargajiya, wadanda su kuma zasu tattauna da matasa, domin saurarar bukatun matasa.”

A nata bangaren mataimakiyar Shugaban Majalisar ɗinkin duniya Amina ta ce, ta zo Najeriya ne tare da tawagarta domin nazarin wasu kalubale da majalisar ta damu da su, musamman annobar korona, sauyin yanayi, tsaro, da sauransu.

Labarai Makamanta

Leave a Reply