#EndSARS: Lallai Gwamnati Ta Ɗau Mataki Akan Cutar Da Musulmi Da Aka Yi A Kudu – Gadon Ƙaya

Babban Malamin musulunci a Jihar Kano ya shawarci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin gaggawa game da zaluncin da masu zanga-zangar SARS suka yi wa musulmi ‘yan Arewa mazauna kudancin Nijeriya.

“Muna kira da akai tallafin gaggawa ga musulmin Fatakwal don suna cikin tsanani, musulminmu na Imo da wanda suke Fulato, da na Aba, da sauran garuruwa, su ma suna bukatar taimako domin suna cikin bala’i, masu wannan zanga-zanga suna son juyar da ita zuwa fada da musulunci, to jami’an tsaro su sani mu ma Wallahi da karfinmu, ba za mu bari a karar da mu ba”.
Inji Sheikh Abdallah.

“Idan da gaske zanga-zangar kawo sauyi ake me yasa duk kashe al’umma da ake a Maiduguri ba su fito tuntuni sun yi wannan zanga-zanga ba? Me ya sa ba su yi ta ba sanda Katsina ta gagara shiga? Ga Sokoto, ga Birnin Gwari nan har yanzu ba a iya shiga ko Soja ko Dan sanda tsoro ya ke ya bi, me yasa ba su yi zanga-zanga akan haka ba? Mutane nawa aka kashe mana?

Yau an wayi gari Dan Kudu shi ne mutum a Nijeriya, mutum d’aya kawai aka kashe aka yi zanga-zanga aka ce sai an kawar da wannan SARS din, kuma shugaban kasa ya sa hannu aka kawar da ita, mu mun san wani SARS ne? Ba su mana komai ba, tunda an dakatar da jami’an mene na cigaba da zanga-zanga? Mene na kone-kone da sace-sace da karkashe musulmi aka kone musu dukiyoyi? Muna gudun abin da rashin daukan mataki ka iya haifarwa na fitina, domin kar hakan ya ingiza mutanenmu su tashi su ce su ma ba su yarda ba”

Kamata ya yi ace gwamnati tafi kowa sanin garuruwan da ake kashe musulmi, kamata ya yi a kai musu agaji sai hankali ya kwanta, amma yau, gobe, jibi, gata, ana ta waya ana kuka an kashe mana wane, an kashe mana wane, an kashe mana wane, kuma shiru mu ke ji ba a tsayar da abun ba, wallahi wannan zalunci ne, shi ya sa wasu ba sa tausayawa abin da ke faruwa saboda sun ga akwai zalunci da rauni”, Cewar Dr Abdallah Gadon kaya.

Tuni aka sami rahotonnin da ke bayyana yadda aka salwantar da rayukan ‘yan Arewa da dukiyoyinsu a wannan tarzoma, sai dai da yawa ba su ji dadin rashin nuna damuwa da gwamnatin tarayya ta yi ba game da hakan, musamman a daidai lokacin da tayi jaje ga al’ummar Legas wadanda suka rasa rayukansu, kuma ta sha alwashin biyansu diyya wanda haka ya kamata gwamnati ace ta yi wa musulman da aka kashe aka kona musu dukiyoyi, tunda su ma ‘ya ‘kasa ne.

Labarai Makamanta

Leave a Reply