EndSARS: Kimanin Fursunoni 2000 Suka Arce Daga Kurkuku

Hukumar kula da gidajen gidajen Yari ta Najeriya (NCS) ta tabbatar da cewa kimanin fursunoni 2000 sun tsere daga gidan yarin da ma su zanga-zanga su ka balle ranar Litinin a Benin, jihar Edo.

An ruwaito yadda wasu batagarin matasa su ka balle wani gidan yari da ke kan titin Sapele a birnin Benin da safiyar ranar Litinin, suka saki fursunonin dake ciki.

Sakamakon hakan, gwamnatin jihar Edo ta sanar da saka dokar ta baci ta sa’a 24, a fadin jihar sakamakon fargabar abin da zai je ya dawo.

A cikin wani jawabi da Hukumar gidajen Yarin ta fitar ranar Talata ta hannun darektan yada labarai da hulda da jama’a, Mohammed Manga, hukumar ta bayyana cewa ”ma fi yawan ma su laifin da su ka tsere wadanda ke jiran a zartar musu da hukuncin kisa ne bayan an yanke mu su hukunci.

“Ma su zanga-zanga a karkashin tutar ENDSARS sun kai hari kan wasu gidajen yari biyu; daya a birnin Benin, daya a Oko, a jihar Benin tare da sakin fursuna 1,993 tare da lalata kayayyaki da suka hada da makaman da ke ajiye a dakin adanasu.

“Matasan na da yawan gaske, sannan su na dauke da makamai ma su hatsari. Ba su boye niyyarsu ta balle dakuna domin sakin ma su laifi ba, kuma sun aikata hakan bayan sun zane jami’anmu da ke kan aiki a lokacin da fatar dorina.

“Sakin ma su laifin hatsari ne ga tsaron kasa, lafiya da dukiyoyin jama’a. Ba za mu yarda da irin wannan hali ba, tuni mun fara bincike domin gano dukkan barnar da aka tafka yayin harin da aka kai gidajen yarin”.

Labarai Makamanta

Leave a Reply