EndSARS: Kar Ka Yi Amfani Da Soji Wajen Daƙile Zanga-Zanga – Atiku Ga Buhari

Tsohon Mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana kaduwar sa da rasa rayukan da aka samu wajen zanga-zanga kan cin zarafin da jami’an ‘yan sanda ke yi wa fararen hula, wanda yace wa su bata gari sun mamaye.

A sakon da ya aike ta shafin sa na Facebook, Atiku ya bukaci gwamnatin Muhammadu Buhari da kar ta amince da shawarar amfani da karfi wajen murkushe masu zanga zangar.

Tsohon mataimakin shugaban ya bayyana masu zanga zangar a matsayin masu hankali dake da aniya mai kyau ga kasa, inda yake cewa yanzu lokaci ne na amincewa da kuma aiwatar da bukatun su.

Abubakar ya ce lokacin da gwamnati ta nunawa ‘yan kasa ta damu da su, a lokacin su kuma suke nuna mata kauna, inda ya bukaci shugaban kasa da ya yi wa jama’ar kasa jawabi, musamman matasa.

Labarai Makamanta

Leave a Reply