EndSARS: Gwamnan Imo Ya Roƙi ‘Yan Kasuwar Arewa Su Koma Jihar

Gwamnan jihar Imo Hope Ezodimma ya yi kira ga yan Kasuwar arewacin kasar nan masu kai kayan abinci zuwa kudancin kasar da su yi hakuri su cigaba da harkokinsu, biyo bayan yadda kayan abinci ke tashin gauron zabi a wannan yankin,

Sulaiman Ibrahim Sulaiman wanda shi ne mai bada shawara ga gwamna Imo akan yan arewacin kasar nan, kuma shi ne ya jagorancin tawagar al’ummar yankin zuwa Kaduna, ya ce sunce sun tuba da wancan muguwar barna da suka yi na cinnawa kayan abincin Hausawa yan Arewa wuta,

Ya kara da cewa “zuwan da nai Kaduna shi ya ce in zo ba don komai ba, sai don matsaloli da aka shiga acan na rashin abinci komai ya fara yin tsada shi ne ya ce na zo na sami mutanenmu na ba su hakuri”

In dai baa manta ba a mako biyun da ya gabata wasu daga cikin yan zanga zangar Endsars suka buge da farwa dukiyoyi da manyan motocin Hausawa a wasu jahohin yankin kudu, alamarin da ya jawo karancin kayayyakin abinci yankin wanda da dama daga arewa a ke kai masu, masu iya magana dai na cewa, Wuya ko tana da magani ba ta da dadi..

Labarai Makamanta

Leave a Reply