#EndSARS: Clinton Ta Gargaɗi Buhari Kan Kashe Masu Zanga-Zanga

Tsohuwar ‘yar takarar shugabancin kasar Amurka, Hillary Clinton ta gargadi shugaba Buhari da ya daina Kashe mutanen kasar sa ta hanyar saka sojoji suna harbin su a wajen zanga-zanga.

Clinton ta rubuta a shafinta ta tiwita cewa ” Ina kira ga Buhari da rundunar Sojin Najeriya da su daina kashe matasa masu zanga-zangar #EndSARS a Najeriya.

” Abinda aka yi wa masu zanga-zangar #EndSARS ya wuce misali, ina kira ga gwamnatocin duniya da majalisar Dinkin Duniya su sa baki akan abinda ke faruwa a Najeriya.

” A daren Talata an samu rahoton yadda sojojin Najeriya suka bude wa masu zanga-zanga wuta a Legas. A bayanan da suka fito bayan wannan arangama sun nuna cewa akwai mutum bakwai da suka rasa rayukan su sannan wasu da dama sun samu raunuka a jikin su.

Ku kasance da shafin mu www.muryaryanci.com domin samun labarai akan abubuwan dake faruwa a fadin kasar nan.

Labarai Makamanta

Leave a Reply