Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya koka da halayyar wasu kafafen yada labarai na kasashen ketare a kan yadda suka yada labaran da suka shafi zanga-zangar EndSARS ta hanyar cakuɗa ƙarya da gaskiya domin cimma wata manufa.
A cikin wani sako da shugaba Buhari ya wallafa a shafinsa na tuwita, ya ce kafafen yada labarai na ketare, musamman CNN da BBC sun sanya son zuciya da ƙoƙarin haddasa fitina a rahotannin su, inda suka yi amfani da bangare guda wajen yada labaran da suka shafi zanga-zangar.
“Wasu kafafen yada labarai na ketare sun wallafa rahotannin cewa dakarun soji sun budewa fararen hula wuta yayin zanga-zangar EndSARS, musammam a yankin Lekki da ke jihar Legas, wanda hakan ƙarya ne muraran”.
Indai jama’a basu manta ba tun a wancan lokaci gwamnatin tarayya, ta fito ta musanta labarin zargin cewa jami’an tsaro sun kashe fararen hula.
Hasali ma, gwamnati ta ce ita aka yi wa barna, saboda an kashe ‘yan sanda tare da kona ofisoshinsu da gidan yari duk da sunan zanga-zanga EndSARS.
“Dole a fadi cewa kafafen yada labarai na ketare ba su yi adalci ba a labaran da suka yada yayin zanga-zangar ENDSARS, musamman daga CNN da BBC. Ban ji dadin labaran da su ka yada ba, wanda ko kadan bai ambaci cewa an kashe jami’an ‘yan sanda ba, an kona caji ofis, an balle gidajen yari”.