A cigaba da yinkurin kamo bakin zaren daidai tawa da matasan Najeriya kan rikita-rikitar zanga zangar kawo karshen cin zarafin yan Najeriya da ake zargin hukumar yan’sanda na bangaren dakile ayyukan yan fashi da makami da ake kira (SARS) wanda ya rikide ya koma tashin tashina.
A jiya litinin ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jinjina wa matasan jihar Bauchi kan irin zurfin tunanin su na kin shiga cikin zanga zanga EndSARS, ya fadi hakan ne a taron tattaunawa da matasa da masu ruwa da tsaki na al’ummar jihar kan hidimar tsaro da gwamna Bala Mohammed tare da hadin gwiwar ministocin da suke wakiltar jihar a majalisar shugaban kasa
Inda zanga-zangar ta rikidi ta jawo asarar rayuka da dumbin dukiyoyin al’umman Nageriya wadanda basuji ba, basu gani ba, yace yana al’fahari da matasan jihar kan nuna halin dattako da kuma hangen nesa.
Shagaban kasan wanda ministan Ilimi Malam Adamu Adamu ya wakilce shi a wajen taron tare da karamar ministan kasuwanci da saka hannun jari, Ambasada Hajiya Maryam Yelwaji
Buhari yace gwamnatin sa tana cigaba da samu sabbin dabaru ta yadda zata rage ma matasan radadin zaman kashe wandu ta hanyar daukan su ayyuka a matakai daban daban da kuma tallafi na sana’oi kala kala.
Yace “babban burin gwamnatinmu, shine samar da tsaro ga kowani dan Najeriya, tare da tabbatar da ingancin jami’an tsaro a fadin Najeriya, da kuma habbaka tattalin arzikin kasa da kowa zaici gajiyar hakan”
Shugaba Buhari ya jinjina wa gwamnan jihar Bala Mohammed da namijin kokarinsa ba a samu tashe tashen hankali na zanga zangar ba, saboda wanzuwar zaman lafiya a jihar Bauchin, yace wan nan kadai gwamnan ya chanchanci a yaba masa.
Gwamnan jihar Bala Abdulkadir Mohammed yayin da yake jawabinsa, yace wan nan taro yanacda matukar muhimmanci, bama a bangaren tarayyab har ma a matakin jiha, yana da kyau shuwagabnni su rika zama da al’ummarsu lokaci zuwa lokaci domun samun mafita kan matsalolin rayuwar mutane tare da share masu hawaye.
Yace “gwamnatin jiha tana aiki kafada da kafada jami’an tsaro da kowa da kowa ba tare da nuna ban bancin Jamiyya ba ko bangaranci, kuma haka mukeyi a jihar mu domin samun ci gaba da zaman lafiya mai dorewa”
Taron ya samu halartan masu ruwa da tsaki kama daga kungiyoyin matasa, da kungiyoyin mata da Sarakunan gargajiya, da jami’an tsaro yan’ siyasa ciki da waje, kuma an saurari bayanai da korafi na matasa, wanda ministan Ilimi Adamu Adamu ya tattara zai kaiwa shugaban kasa.
Daga Adamu Shehu Bauchi