Fadar shugaban kasa ta yi kira na musamman ga yan Najeriya dasu kwantar da hankalin su a daidai lokacin da ake ci gaba da aiwatar tsare-tsaren garambawul ga aikin ‘yan sanda a matakin tarayya da jihohi.
Wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasar kan yada labarai Femi Adesina ya fitar a ranar Laraba, ya jaddada kokarin gwamnatin kasar na aiwatar da kwararan matakai da za su inganta aikin dan sanda a fadin kasar.
Ya ce shugaba Buhari ya yi maraba da kafa kwamitin bincike da jihohi 13 suka yi, kan zargin saba ka’idojin aiki da ake yi wa yan sanda.
Jihohin da suka kafa kwamitin sun haɗa da Lagos, Kaduna, Delta, Ekiti, Ogun, Anambra, Enugu, Imo, Plateau, Edo, Nasarawa, Ondo da Akwa Ibom.
Buhari wanda ya yaba da wannan mataki na jihohin, ya kuma bada tabbacin gwamnatinsa na tallafa wa jihohin don samar da adalci ga duk waɗanda abun ya shafa na muzgunawar ‘yan sanda a faɗin kasar.
A wani labarin kuma da safiyar yau jaridar Muryar ‘yanci ta kawo maku ruhoton yadda wasu da ake zargin matasan dake zanga Zangar EndSars sun kona gidan talbijin na TVC dake legas. Hakan yasa tajwaranta Channels TV ta kulle gidan talbijin dinta amman daga baya sun dawo domin cigaba da gudanar da shirye shiryen su kamar yadda suka saba.
Ku kasance da shafin mu na www.muryaryanci.com domin samun sahihan labarai akan abubuwan dake faruwa a fadin kasar nan.