Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya roki matasa da su daina zanga-zanga a tituna, su yi kokarin tattaunawa mai amfani da gwamnati da nufin gyara domin dakatar da zalincin da ‘yan sanda ke yi wa ‘yan Najeriya.
Shugaba Buhari ya nuna rashin amincewarsa da amfani da karfi da matasa ke yi wurin tayar da tarzoma ga ‘yan Najeriya da ba su ji ba, ba su gani ba, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa.
Yayi wannan rokon ne a wata takarda da ya fitar don murnar zagayowar ranar matasa wacce ake yi duk ranar 1 ga watan Nuwamba, wacce kuma ta yi daidai da ranar matasan Afirika.
Idan ba a manta ba, matasa sun yi zanga-zanga a kan rundunar ‘yan sandan SARS a makonnin da suka gabata, wanda hakan yayi sanadiyyar rushe rundunar.S
Shugaban kasar da ya samu wakilcin ministan Abuja, Muhammad Bello, ya ce, ya ji duk abubuwan da matasa ke rokonsa da ya aiwatar, kuma ya ce kada su ji tsoron fitowa fili don tattaunawa da gwamnati don kawo canji a ayyukan ‘yan sanda.