EndSARS: Babu Wanda Soji Suka Harba A Lekki – Rundunar Soji

Kwamandan Bataliya ta 65, ta rundunar sojojin Najeriya Salisu Bello, ya fito fili ya ?aryata batun zargin aikata kashe-kashen da ake yi wa sojoji a Lekki Tollgate.

Kwamanda Salisu Bello yace ko ka?an wannan labarin bai inganta ba, domin har ruwa da ruwan lemu sojoji suka gabatar wa da masu zanga- zangar EndSARS don Karamci, Sannan duk karar harbi da aka ji a Lekki, sojoji sun yi ne a sama ne don tsoratar da masu zanga-zangar.

Masu zanga-zangar EndSARS sun kai wa sojoji hari a Lekki Toll gate ranar 20 ga watan Oktoba 2020 a gaban jama’a da rana ?iri-?iri.
Kwamandan yayi ikirarin hakan a wata takarda da ya gabatar wa kotu dangane da harbe-harben da aka yi a Lekki.

Gwamnatin jihar Legas ta samar da wata kwamitin da zai yi bincike tukuru a kan kashe-kashen, inda take tunanin hakan ne zai kawo zaman lafiya a jihar.

Bello, wanda ya musanta kashe-kashen da aka alakanta da sojoji a Lekki toll gate ya ce masu zanga-zangar sun yi farincikin ganinsu. Kwamandan sojin ya kara da cewa, har ruwa da ruwan lemu suka mika wa masu zanga-zangar, suna masu rokon su da subar wurin, su koma gidajensu.

A cewarsa, yayin da ya tunkari babban titin Lekki-Ajah wuraren 6:45 na yamma, ya ji karar harbe-harbe wuraren tollgate, ya hango masu zanga-zangar lumanar a hargitse. Yana isa wurin ya fara rokon jama’an da su koma gidajensu gwamnatin jihar ta sanya kullen awanni 24, kawai sai jama’a suka kwashi duwatsu, kwalabe da sauran miyagun makamai suna jifaf sojoji, har su na kona tayoyi, a cewarsa.
“Har harbi na yi a sama, don in tsoratar da su. Amma wasu daga cikin masu zanga-zangar da na bai wa ruwan lemu da ruwa don su tafi, suka cigaba da zama a bakin gate din.” Ya ce harbin da sojoji suka yi, a sama suka yi. Sannan ya musanta kashe-kashe da boye gawawwaki da mutane suka yi ta ikirari sojoji sun yi.

Related posts

Leave a Comment