#EndSARS: Ba A Kashe Wuta Da Wuta – Sheikh Bauchi

Fitaccen Malamin addinin musulunci kuma babban jigo a Darikar Tijjaniyya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya shawarci gwamnatin Nijeriya da ta shawo kan rikicin zanga-zangar da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

Malamin ya ce” Ya kamata masu wannan zanga-zanga su dakatar da ita, domin idan wannan lamari ya cigaba da tafiya a haka komai zai iya lalacewa, abun da aka raina na zaman lafiya shi ma sai a rasa shi.”

Ya kara da cewa” Muna janyo hankalin gwamnati da ta lura da hakkin jama’ar kasa mu na fatan a sami wadanda za su fada mata gaskiya ta karba, bai kamata a bar abubuwa suna tafiya kamar haka ba, lamarin ba zai haifar da d’a mai ido ba.

“Ba a kashe wuta da wuta, da ruwa ake kashe wuta. Ya na da kyau gwamnati ta saurari korafin mutane ta biya musu bukatunsu.

Gwamnati ta na da kunne da ido, kuma ta san abun da ke damun al’umma na matsi, yunwa, rashin aikin yi, tsadar rayuwa da rashin tsaro.

Don haka ya kamata gwamnati ta yi kokarin karbar korafe-korafen mutane ta kuma sama musu mafita”, inji Shehin Malamin.

Labarai Makamanta

Leave a Reply