Al’ummar yankin kudancin Nijeriya sun shiga matsanancin tsadar rayuwa, tun bayan da ‘yan kasuwa da manoman yankin Arewa suka dakatar da kai kayayyakinsu yankin, sanadiyyar barnar da suka yiwa ‘yan Arewa a lokacin Zanga-zangar #ENDSARS.
Al’ummar yankin sun shiga kuka saboda bala’in tsadar rayuwa, inda kayan miya da nama suka yi masifar tsadar da basu taba yi ba, saboda babu kayayyakin a kaf yankunan, hakan ya faru ne sakamakon yanke huldar kasuwanci da manoma da ‘yan kasuwar Arewa su kayi saboda zargin kashe masu mambobi da kona dukiyoyin su da akayi a yankin lokacin zanga-zangar.
EndsarsA binciken da aka yi an kashe akalla mutum fiye da 17 an kona trelolin kayan miya akalla 74 sannan an kona shagunan masu sayar da kayan miya akalla shaguma 104 na ‘yan Arewa dake zaune a kudu.