EndSARS: An Ƙona Gidan Talabijin Na TVC

Wasu da ake zargin yan daba ne sun kai hari kan gidan talabijin na TVC da ke Ketu a jihar Lagos.

Shaidun gani da ido sun ce sun bayyanawa wakilin Jaridar Muryar ‘Yanci yadda ‘yan dabar suka kona kayan aiki da motocin wurin.

Wani ma’aikacin TVC ya shaida wa Muryar Yanci cewa wasu daga cikin ma’aikatan da harin ya rutsa da su, sun tsallake rijiya da baya.

Tashar TVC dai ana alakanta ta ne da tsohon gwamnan jihar Lagos kuma jagoran jam’iyyar APC na ƙasa Bola Tinubu kuma da dama sun bayyana cewar mallakan Tinubu ne.

A baya bayan nan dai Zanga-Zangar EndSARS ta kara tsami a wasu Jihohin ƙasar, inda a makon da ya gabata ne ma, masu Zanga-Zangar suka ɓalle gidan Yarin Benin inda suka saki dimbin ‘yan gidan kurkuku, baya ga ga sauran dukiyoyon jama’a da aka ɓarnatar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply