#EndSARS: Ƙungiyar Kudancin Najeriya Ta Yaba Matasan Arewa

Ƙungiyar tabbatar da zaman lafiya ta yankin Kudu Maso gabashin Najeriya, sun yaba gami da jinjinawa matasan Arewa, bisa ga matsayin da suka ɗauka na zaman lafiya lokacin Zanga-Zangar EndSARS.

Kungiyar Zaman lafiyan Kudancin ta koma yi kira ga gwamnonin Arewa da su kara kaimi wajen samar da wani yanayi na tuntubar matasan Arewa a duk lokacin da wani al’amari ya bijiro.

Bayanin hakan na ƙunshe ne a cikin wata takardar sanarwa da ta samu sanya hannun shugaban kungiyar Dr Obi Chibuzor da mai ba Ƙungiyar shawara ta fuskar Shari’a Barista Amadi Ojukwu, kuma aka rarraba ta ga manema labarai.

“Akwai wasu labaran ƙanzon kurege da ke yawo a kafafen sadarwa na zamani na cewar wai Matasan Inyamurai sun kaddamar da hari akan ‘yan arewa mazauna kudanci, amma abin farin ciki tuni matasan na Arewa suka yi watsi da wadannan labaran ƙarya suka rungumi zaman lafiya a yankin arewa, lallai wannan abin a yaba ne inji su”.

Kungiyar Kudancin Najeriyar sun kara da cewar lalle ne ya zama wajibi ga dukkanin jama’ar Najeriya musamman Matasa su tashi tsaye su kawar da dukkanin wasu maganganu na kyamatar juna da wasu miyagu ke kokarin haddasawa tsakanin ‘yan Najeriya walau ta banbancin addini ko yanki.

Dangane da kalaman da shugaban tsagerun kungiyar Inyamurai Nnamdi Kanu ya yi kwanan nan akan tayar da hankali musanman a jihar Legas, Ƙungiyar zaman lafiyar ta kudu ta yi kira ga jama’a da suyi watsi da wannan magana, domin Kanu yana magana ne a ƙashin kanshi ba da yawun Inyamurai ba.

Labarai Makamanta

Leave a Reply