Sanata mai wakiltan maza?ar Kaduna ta arewa, a majalisar Dattawa Suleiman Abdu Kwari, ya taya sabon sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli murnar nada shi a matsayin sarki da gwamnatin jihar Kaduna ta yi.
Yayinda yake jinjinawa karfin gwiwa da hikimar da ke tattare da zabar Bamalli da Gwamna Nasir El-Rufai yayi domin ya maye gurbin Marigayi Shehu Idris, Sanatan ya yaba da hakuri da juriyar ‘yan gidan sarautar Mallawa na fiye da shekaru 100.
Da yake tuna cewa Malam Musa na gidan sarautar Mallawa ne ya kafa masarautar Fulanin Zazzau, Kwari ya ce gidan sun rasa sarautarsu tsawon shekaru sama da 100.
“Lallai Gwamna El-Rufai ya yi aiki da hikima da karfin zuciya wajen tabbatar da cewar an zabi dan takarar da ya cancanta a sati biyu da aka yi ana takara.
“Yayinda muke shiga sahun masu taya sabon Sarki da gwamna murnar sauke nauyin da ya rataya a wuyansa, muna kira ga ‘yan uwanmu Zaga Zagi da su ba sabon sarki hadin kai sannan su hada hannu wajen ci gaban masarautar” in ji sanatan.
Sanata Kwari ya bayyana cewa shakka babu mutanen Zaria, cibiyar ilimi, sun yi imani da cewar mulki na Allah ne kuma Shi ke baiwa wanda Ya so.