El Rufai Bai Tauye Hakkin Addinai Ba Lokacin Mulkin Sa- Imam Bukhari Maraban Jos

SHUGABAN kwamitin tsangayu na jihar Kaduna, Imam Bukhari Maraban Jos ya maida martani ga masu cewa kada a nada tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir Ahmad El-Rufa’i a matsayin minista.

Shehin Malamin ya yi wannan martani ne yayin da ya ke zantawa da manema labarai a yau Litinin, 31 ga Yuli, 2023.

Imam Bukhari ya ce, “Mun wayi gari, mu ka ga wani rubutu da wani ya yi game da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai.

Mu a matsayin mu, mu na martaba gidan Shehu, kuma mu na yarda da duk abin da ya zo mana daga gare shi, saboda matsayin sa a addini. Amma wannan ba zai hana wasu ko wani ba ya yi amfani da rigar gidan Shehu su cusa kan su cikin siyasa don su cutar da wani saboda manufar su ta siyasa.”

Imam ya ci-gaba da cewa, “Alhamdu lillah kowa ya sani, wasu daga cikin su sun fito sun bayyana ra’ayoyin su kan dan takarar da su ke so a zaba, yanzu kuma Allah ya ba ma wadanda ba su yi daidai da ra’ayoyin su ba, don haka ba daidai bane yanzu wani ya fito ya ce wai kada a ba wa Malam Nasir El-Rurai mukamin minista, saboda wai El-Rufai bai da abin fada a jihar Kaduna. In ya ce haka bai taimaki addini ba, ko bai taimaki almajirci ba, wannan ra’ayi ne, in bai gani ba da yawa sun gani.”

Sannan kuma, maganar almajirai a jihar Kaduna, abubuwan da su ka faru a baya, an zauna da mai girma gwamna da shi Malam Albani, an wuce wannan wurin. Ba daidai ba ne a dawo da maganar baya, domin a cimma wata manufa na siyasa.

Alhamdu lillah. Bayan maganar almajirai ta kauce, alkhairai da yawa sun biyo baya, don har sai da aka gina makarantun tsangaya 25 a fadin jihar Kaduna, bayan maganar korar almajirai, a yanzu haka ana gina tsangayu 11 wanda kowanne zai lakume N7,000,000.

Hukumar kula da ilimi matakin farko ta tarayya (UBEC) tare da hadin gwiwar hukumar kula da ilimi matakin farko na jiha (SUBEB) ke gina wa.

Ba daidai ba ne a baya kun nuna ba ku tare da su (APC) kafin zabe, yanzu kuma Allah ya ba su nasara ku fara kalubalantar su.

Don haka, ba za mu lamunta ba, wani ya yi amfani da rigar gidan mutunci ya ci mutuncin shugabanni. Wannan ita ce amanar da ke kan mu, mu fada abin da mu ka sani don kare martabar gidan Shehu.

Ba ka gani, kowa ya na da ‘yancin fadar ra’ayin sa a siyasa.

Duk da cewa, masu sukar su ma ‘yan jihar Kaduna ne su na da ‘yancin fadin ra’ayin su, mu kuma mu na da ‘yancin kare gaskiya.

Mabiya addinin kiristanci sun zargi Malam Nasir El-Rufa’i da mika wa al’ummar musulmi hakkin su. Yanzu kuma ga wasu Malamai su na kalubalantar tsohon gwamnan da tauye wa musulmi hakki.

An tambayi Imam ko me zai ce game da hakan? Sai ya amsa da cewa “Wannan siyasa ce kawai. Sun bayyana ra’ayin su a kan Jam’iyyar PDP, mu kuma mun bayyana ra’ayin mu a kan Jam’iyyar APC. Don haka, duk bangarorin biyu ra’ayi ne na siyasa kawai.”

Da aka tambaye shi, a matsayin sa na wanda ya yi aiki a karkashin Malam Albani, me zai fada al’ummar Nijeriya in Allah ya tabbatar Malam Nasir El-Rufa’i da wannan matsayi na minista? Sai ya ce, “Duk lokacin da aka ce kai shugaba ne, dole sai wani ya ga ba a yi masa daidai ba. Abin da ya fi dacewa da al’umma shi ne; addu’a ga shugabanni don samun nasara.

Malam Nasiru El-Rufai dan adam ne wanda zai iya kuskure kuma mu na rokon Allah ya yafe masa kurakuran sa, amma ya yi aiki matuka a jihar Kaduna.

Labarai Makamanta

Leave a Reply