Hukumar EFCC ta sanar da cewa a ranar 9 Ga Janairu za ta yi gwanjon wasu kadarorin da su ka haɗa da manyan gidaje, filaye da fulotan da ta ƙwato daga yawancin ɓarayin gwamnati da kuma mazambata.
Za a yi gwanjon kadarorin ne a ranar 9 Ga Janairu, 2023, a dandalin taron yaye ɗalibai na Jami’ar NOUN da ke maƙwautaka da Hedikwatar EFCC.
Kakakin EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana haka a cikin wata sanarwar da ya fitar a ranar Laraba.
Haka nan kuma EFCC ta umarci dukkan masu son shiga neman sayen kadarorin ya aika wa hukumar da buƙatar sa a rubuce nan da ranar Litinin, 9 Ga Janairu, 2023 sannan a bi nan efcc.gov.ng
Idan ba a manta na, Shugaban EFCC AbdulRashid Bawa dai tun a ranar 16 Ga Disamba ya sanar cewa nan ba da daɗewa ba hukumar sa za ta fara sayar da kadarorin da ta ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati a, faɗin ƙasar nan.
Ya faɗi cewa za a koma sayar da kadarorin ne na gidaje, fulotai da filaye masu yawa bayan kammala sayar da motocin da aka ƙwato daga hannun ɓarayin gwamnati.