Site icon Muryar 'Yanci – Labaru, Siyasa, Tsaro, Lafiya, Ilimi…

EFCC: Za A Rasa Masu Ƙarfin Gwiwar Yaƙi Da Rashawa A Najeriya – Osinbajo

Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, ya yi hasashen cewa nan bada dadewa ba yaki da cin hanci zai kara zama abu mai matukar wuyar gaske. Ya ce za a kai ga matakin da jama’a da yawa zasu rasa karfin gwuiwar mikewa domin yakar cin hanci da rashawa.

Osinbajo ya bayyana hakan ne a cikin jawabin da ya gabatar yayin wani taro da hukumar ICPC mai yaki da cin hanci a tsakanin ma’aikata da masu rike da mukaman gwamnati ta gudanar ta hanyar amfani da fasahar yanar gizo.

Kakakin Osinbajo, Laolu Akande, ne ya raba kwafin jawabin mataimakin shugaban kasa ga manema labarai a ranar Talata. “Yaki da cin hanci yana fuskantar tarnaki, kullum kara wahala yake yi; maganar gaskiya, yaki da cin hanci zai cigaba da kara wuya ta yadda mutane da yawa zasu rasa karfin gwuiwar mikewa domin yaki da cin hanci.

“Amma, duk da haka, alhakinmu ne a matakin mutane da hukumomi, musamman a kasashe masu tasowa, mu tashi tsaye domin bawa yaki da cin hanci fifiko tare da cigaba da bullo da sabbin hanyoyin dakile wannan babbar barazana.

Osinbajo ya bayyana cewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta nuna cewa a shirye ta ke domin yaki da cin hanci, lamarin da yasa gwamnati ta bawa hukumomin yaki da cin hanci damar yin aikinsu ba tare da katsalandan ba.

A makon jiya ne wasu kafafen yada labarai suka wallafa cewa Magu ya sanar da kwamitin da ke bincikensa cewa ya bawa Osinbajo biliyan N4 daga kudaden da aka kwace a hannun mabarnata. A cewar rahotannin, Magu ya sanar da kwamitin cewa ya ba Osinbajo kudin ne bayan ya nemi a sakar ma sa wani bangare na kudaden da EFCC ta kwace.

Sai dai, a cikin wani jawabi da Akande ya aikewa manema labarai ya bayyana wadancan rahotanni a matsayin na ‘kanzon kurege’ da babu gaskiya a cikinsu. Kafar yada labarai ta yanar gizo, PointBlank, mallakar Jackson Ude; wani tsohon hadimin Jonathan, ta wallafa rahoton cewa Magu ya barnatar da biliyan N39 tare da bawa Osinbajo biliyan N4 daga cikin kudin a matsayin toshiyar baki.

A ranar Laraba, 6 ga watan Yuli, ne Osinbajo ya rubuta takardar korafi zuwa ofishin babban sifeton rundunar ‘yan sanda na kasa (IGP), Muhammad Adamu, domin neman a binciki ma su alakanta shi da karbar kudi daga hannun Magu.

A cikin wasikar da Osinbajo ya rubutawa IGP ta hannun lauyansa, Taiwo Osipitan, ya bayyana rahoton a matsayin kage da sharri domin bata ma sa suna, a saboda haka ya bukaci a bi ma sa hakkinsa.

Exit mobile version