EFCC Ta Sake Bankado Zunubban Tsohuwar Ministar Mai

Hukumar EFCC ta ce binciken da ta gudanar ya nuna cewa, Diezani Madueke, tsohuwar ministar albarkatun man fetur, ta bai wa ‘yan siyasa dala miliyan 115 domin yin magudin zaben shekarar 2015.

Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ne ya bayyana haka a ranar Laraba nan a wani taron karrama sabbin kwamishinonin zabe (INEC) da aka yi a Legas.

Bawa wanda ya samu wakilcin Adukwu Michael baban darakta a hukumar mai kula da sashen binciken laifuka, ya bayyana wannan rashin gaskiya da tsohowar ministar ta aikata a matsayin babban abin takaici kuma cin amanar kasa ne.

Diezani ta kasance ministar albarkatun man fetur daga shekarar 2010 zuwa 2015 a lokacin gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan. Tsohuwar ministar dai ta bar kasar nan ne kwanaki kadan kafin Jonathan ya mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari mulki a 2015 .

Ana zargin tsohuwar ministar da sace dala biliyan 2.5 daga asusun gwamnatin Najeriya a lokacin da take ofis. Sai dai ta musanta zargin. Daga shekarar 2016 zuwa yanzu EFCC tayi nasarar kwace kadarorin Diezani wanda suke hada da rukunin gidaje a Banana Island a jihar Legas da wasu gidaje a abuja.

Yayin da yake bayani game da batun tsohuwar ministan wakilin shugaban EFCC ya ce hukumar ta kwato wasu daga cikin kudaden da ake zargin Diezani ta sace.

“Hukumar EFCC ta maida hankali wajen shirya taruka da bitoci dan wayar da kan al’ummar illar siyar da kuri’a da kuma nakasun da zata kawo” “Sau da yawa jam’iyyu ba siyan kuri’au masu zabe da kudi saboda ba su da ingantattun tsare-tsare da za su gamsar da masu zabe su zabe su a mulki.

Labarai Makamanta

Leave a Reply