Rahotanni sun bayyana cewa an yi harbe-harbe a wannan Larabar yayin da Gwamnan Kogi, Usman Ododo, ya tsere da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
Lamarin na zuwa ne yayin da Ododo ya kai ziyara gidan Yahaya Bello da ke titin Benghazi a Unguwar Wuse Zone 4 da ke Abuja.
An ruwaito yadda jamian Hukumar Ya?i da Yi wa Tattalin Arzikin ?asa Taannati (EFCC) suka yi wa gidan Yahaya Bello ?awanya tun da misalin ?arfe 9:25 na safiyar Laraba da nufin kama shi.
Sai dai jamian na EFCC tare jamian tsaro da suka ha?a da yan sanda da DSS sun shafe saoi ba tare da sun tabbatar da cika aikin nasu ba.
An samu rahoton cewa suna shirin kama shi da ?arfin tsiya kafin isowar Gwamna Ododo, wanda ya shiga cikin gidan Yahaya Bello tare da ?imbin masu zanga-zangar suna rera wa?o?in nuna goyon baya ga yadda jamian suka yi wa gidan ?awanya.
Sai dai a yayin da Gwamna Ododo ke barin gidan, Aminiya ta samu rahoton cewa Yahaya Bello na cikin motarsa, lamarin da ya tilastawa jamian tsaron da suka kwashe saoi a cikin shirin bu?e wuta.
Masu zanga-zangar, da yan jarida da masu kallo da masu wucewa sun yi ta tururuwa don kare lafiyarsu a lokacin da jamian ke harbin.