Rahotanni sun bayyana cewa an yi harbe-harbe a wannan Larabar yayin da Gwamnan Kogi, Usman Ododo, ya tsere da tsohon gwamnan jihar, Yahaya Bello.
Lamarin na zuwa ne yayin da Ododo ya kai ziyara gidan Yahaya Bello da ke titin Benghazi a Unguwar Wuse Zone 4 da ke Abuja.
An ruwaito yadda jami’an Hukumar Yaƙi da Yi wa Tattalin Arzikin Ƙasa Ta’annati (EFCC) suka yi wa gidan Yahaya Bello ƙawanya tun da misalin ƙarfe 9:25 na safiyar Laraba da nufin kama shi.
Sai dai jami’an na EFCC tare jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda da DSS sun shafe sa’o’i ba tare da sun tabbatar da cika aikin nasu ba.
An samu rahoton cewa suna shirin kama shi da ƙarfin tsiya kafin isowar Gwamna Ododo, wanda ya shiga cikin gidan Yahaya Bello tare da ɗimbin masu zanga-zangar suna rera waƙoƙin nuna goyon baya ga yadda jami’an suka yi wa gidan ƙawanya.
Sai dai a yayin da Gwamna Ododo ke barin gidan, Aminiya ta samu rahoton cewa Yahaya Bello na cikin motarsa, lamarin da ya tilastawa jami’an tsaron da suka kwashe sa’o’i a cikin shirin buɗe wuta.
Masu zanga-zangar, da ’yan jarida da masu kallo da masu wucewa sun yi ta tururuwa don kare lafiyarsu a lokacin da jami’an ke harbin.