Rahotannin da jaridar muryar ‘yanci ta samu yanzu na cewa fadar shugaban kasa ta maye gurbin Ibrahim Magu da Muhammad Umar.
Muhammad shine babban daraktan gudanarwa na hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, kuma shine zai kasance mukaddashin shugaban hukumar kamin daga bisani a nada Wanda zai jagoranci hukumar.
Ibrahim Magu ya shafe shekaru 5 yana jagorancin hukumar a matsayin mukaddashin shugaban hukumar. Sai a ‘yan kwanakin nan wasu tuhume tuhume suka taso akan wasu zargin da ministan shari’a ke masa na almundahanar wasu makudan kudade.