Kungiyar raya tattalin arzikin ƙasashen Afirka ta Yamma Ecowas ta ware dala miliyan 25 da zimmar yaƙi da ta’addanci a ƙasashen Najeriya, da Nijar, da Mali, da Burkina Faso.
Ecowas ta tsara kashe kuɗin ne a shekarar 2024, kamar yadda Kwamashinar Raya Al’umma ta Ecowas Farfesa Fatou Sarr ta bayyana a hedikwatar ƙungiyar da ke Abuja yau Juma’a.
Farfesar ta ce an ware miliyan huɗu daga cikin kuɗin don ayyukan agaji musamman ga mutanen da bala’o’i suka shafa.
“Haka nan, Ecowas ta ware dala miliyan ɗaya da zimmar daidaita rayuwar mutanen da ta’addanci ya shafa, kamar ‘yan gudun hijira da kuma waɗanda aka ji wa rauni,” in ji ta cikin rahoton kamfanin dillancin labarai na NAN.
Ta ƙara da cewa a 2023 kaɗai, Ecowas ta ba da tallafin dala miliyan 12.6 ga mutane sama da miliyan huɗu da ta’addanci ya shafa a yammacin Afirka.