ECOWAS Ta Ba Sojin Da Suka Yi Juyin Mulki A Nijar Wa’adin Mako Guda

Shugabannin kasashen yammacin Afrika sun bai wa sojojin da suka kwace mulki a Nijar wa’adin mako guda da su janye, yayin da kuma suka kakaba wa kasar takunkuman karayar tattalin arziki da kudade.

Kungiyar Bunkasa Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afrika ta ECOWAS mai mambobi 15 sun bukaci a gaggauta sakin shugaba Mohamed Bazoum tare da mayar da shi kan kujerarsa bayan sojojin sun hambarar da gwamnatinsa tare da tsare shi tun ranar Larabar da ta gabata.

Wata sanarwa da ECOWAS ta fitar bayan wani taron gaggawa da ta gudanar a birnin Abuja ta ce, za ta dauki dukkanin matakan da suka dace domin maido da kundin tsarin mulki a Nijar muddin sojojin suka gaza mutunta umarnin kungiyar cikin mako guda.

ECOWAS ta ce da yiwuwar ta yi amfani da karfi daga cikin jerin matakan da ta ce za ta dauka kan sojojin na Nijar da suka yi juyin mulki.

ECOWAS ta sanar da dakatar da daukacin harkokin kasuwanci da kudade tsakaninta da Jamhuriyar Nijar wadda ita ma mamba ce a cikin kungiyar ta yammacin Afrika.

Kazalika ECOWAS ta ce, za ta daskarar da kadarorin Nijar da bankunan kasuwancin kasar tare da haramta wa sojojin da suka yi juyin mulki tafiye-tafiye zuwa kasashen ketare.

Yanzu haka gagarumar zanga-zanga ta barke a babban birnin Yamai, inda fusatattun matasa suka kaddamar da hari kan ofishin jakadancin Faransa, yayin da Faransar ta yi wa masu zanga-zangar gargadi game da kai wa Faransawa hari a kasar.

Labarai Makamanta

Leave a Reply