ECOWAS: Buhari Zai Ziyarci Nijar Yau Litinin

Shugaba Muhammadu Buhari zai ziyarci kasar Nijar a yau Litinin domin halartan taron shugabannin kasan yankin Afrika ta yamma karkashin gammayar ECOWAS.

Mai magana da yawunsa, Malam Garba Shehu, ya bayyana hakan ranar Lahadi, a shafinsa na Tuwita.

Ya ce Buhari zai samu rakiyar manyan ministocinsa kuma zai dawo bayan zaman.

Garba Shehu yace: “Shugaba Muhammadu Buhari zai tashi daga Abuja zuwa Niamey, jamhurriyar Nijar domin halartan taron gangamin shugabannin kasar yankin Afrika ta yamma ECOWAS karo na 57.

A taron da za’ayi cikin kwana daya, za’a tattauna kan rahoto na musamman kan COVID-19 da shugaba Buhari zai gabatar bayan nadashi zakaran yaki da COVID-19 a taron yanar gizon da akayi ranar 23 ga afrilu, 2020.

Hakazalika za’a tattauna kan lamarin ta’addanci, barandanci da kuma juyin mulkin da Sojoji sukayi a kasar Mali.

Labarai Makamanta

Leave a Reply